Jamus tayi adawa da shirin rage iska mai guba na Motoci | Labarai | DW | 19.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tayi adawa da shirin rage iska mai guba na Motoci

Gwamnatin Jamus ta bayyana ɗacin ranta dangane da shirin hukumar kungiyar Tarayyar Turai na gabatar da doka mai tsanani ,domin rage yawan iskar gas mai guba da motoci ke fitarwa.A yayin taro a birnin Brussels,majalisar zartarwar kungiyar ta gabatar da shirin rage yawan iskar gas mai guba da sabbin motocin pasinja ke fitarwa daga gram 160 zuwa 120 a kowace tafiyar km nan da shekarata 2012.Ayanzu abunda ya rage shine kasashen dake kungiyar su amince da batun.Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel ta nuna rashin gamsuwarsa dacewa,rage yawan iskar gas mai guba da motoci ke fitarwa ko kadan bazai dace da harkokin tattali ba,domin hakan zai dorawa jamus da masu kera motocin ta wani karin nauyi.

Ita ma ministar kare muhalli Sigmar Gabriel wadda ke marawa shirin kare muhalli na kungiyar tarayyar turai,da soki wannan tsarin dacewar ,wannan wata alama ce ta nuna kishi da masanaantun kera motoci na jamus,domin cin moriyar kasashen faransa da Italiya dake gasa da ita.