Jamus tace babu ruwan ta da batun shirin kaiwa Iran hari. | Labarai | DW | 18.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tace babu ruwan ta da batun shirin kaiwa Iran hari.

Gwamnatin Jamus ta nesanta kan ta daga ɓanɓarmar da Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner yayi a game da yiwuwar afkawa ƙasar Iran da yaki. Kakakin gwamnatin a birnin Berlin yace Jamus na kokarin ganin an cimma masalaha da mahukunta a birnin Tehran game da taƙaddamar nukiliyar Iran din. A kwanannan ne Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner ya gargadi ƙasashen duniya da su kasance cikin shirin yaƙi da Iran idan har ta mallaki makamin nukiliya. Shima da yake tsokaci Muƙaddashin Ministan harkokin wajen ƙasar Rasha Alexander Losyukov yayi kashedin cewa dukkan wani matakin sojin akan Iran zai kasance babban kuskure da zai iya haifar da mummunan sakamako, yace yana fata taƙaddamar ba zata yi tsammari ba kafin babban taron yankin gabas ta tsakiya da ake shirin gudanarwa a watan Oktoba mai zuwa. Alexander Losyukov ya ja hankali da cewa harin na iya haddasa matsaloli masu yawa ga Amurka.