1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi maraba da manufofin Macron

Yusuf Bala Nayaya
September 27, 2017

Steffen Seibert ya ce Merkel ta yi farin ciki da ganin irin shawarwari da Shugaba Macron ya gabatar da za su taimaka wajen ciyar da Kungiyar EU gaba.

https://p.dw.com/p/2ko93
Frankreich Migrationsgipfel in Paris
Hoto: Reuters/C. Platiau

Mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya bayyana cewa Jamus na nazari cike da fata nagari kan bukatar da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gabatar kan makomar Kungiyar Tarayyar Turai, sai dai ya ce yanzu ya yi wuri a bayyana abin da ke kunshe cikin shawarwarin da shugaban ya gabatar.

Steffen Seibert ya ce Merkel ta yi farin ciki da ganin irin shawarwari da Macron ya gabatar da za su taimaka wajen ciyar da Kungiyar EU gaba, kuma akwai batutuwa da za a sake zama a tafka muhawara a kansu saboda muhimmancinsu.

Har ila yau Seibert ya ce bayan zaben ranar Lahadi Merkel ta yi dogon zama don tattaunawa kan gwamnatin hadaka wacce ba makawa ta ba wa manufofi na kare kudiran Tarayyar Turai muhimmanci.

Macron da Merkel da wasu shugabanni 26 na EU za su zauna wata liyafar cin abincin dare a Estonia a ranar Alhamis kafin taron koli kan makomar ta kasashen Turai idan ana magana ta ci gaban fasahar zamani.