1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi kamen masu fataucin mutane

Ramatu Garba Baba
April 18, 2018

Mutane fiye da 100 ake tsare da su bisa dalilai da suka hada da laifin fataucin mutane ko tilastawa mata aikin karuwanci a wani samame da jami'an tsaro suka kaddamar a sassan kasar.

https://p.dw.com/p/2wI70
Bundesweite Razzia gegen Organisierte Kriminalität
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Vogel

'Yan sandan kasar Jamus akalla dubu daya da dari biyar ne suka shiga wannan aiki a wani abu da ake kallo a matsayin samame mafi girma da aka taba yi a kasar, don magance matsalar fataucin mutane da wasu gungun mutane ke yi tare da bautar da jama'ar da ke da burin zuwa kasar don inganta rayuwarsu. An kama wata mata 'yar asalin kasar Thailand da mijinta Bajamushe da suka yi kaurin suna a wannan sana'a ta shigo da mutane Jamus da takardun boge, kafin daga bisani su tilasta musu shiga aikin karuwanci.

Babbar jami'ar 'yan sanda Martina Dressler ta baiyana takaici kan halin da aka sami mutanen da wasu 'yan tsiraru ke ci da guminsu. Samamen wanda shi ne mafi girma da aka taba gudanarwa a kasar, an yi shi ne da zummar kawo karshen ayyukan wadannan miyagun mutanen da ke wannan aiki.