1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta yafewa Ghana bashin Euro miliyan 270

A lokacin da ya ke bude wani taron kasashen Afirka da na Turai a birnin Accra na kasar Ghana, shugaban tarayyar Horst Köhler ya sanar da yafewa Ghana bashin da Jamus ke bin ta. Yanzu haka dai Jamus ta yafewa Ghana bashin Euro miliyan 270 da take bin kasar ta yammacin Afirka. Taron na samun halarcin shugabannin kasashen Afirka da manyan ´yan kasuwa na wannan nahiya da kuma Jamus. A jawabinsa Köhler ya nunar da cewa:

“Burin mu shi ne mu nunawa ´yan Afirkan cewa muna sauraron su ba tare da nuna bambamci ko nuna cewa muna samansu su kuma suna kasa da mu. Dole ne mu dukkan mu biyu mun gane cewar makomar guda ce a wannan duniya.”