Jamus ta tsallake zuwa wasa na gaba | Labarai | DW | 03.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta tsallake zuwa wasa na gaba

Jamus ta samu nasara akan Argentina a gaban Angela Merkel

default

Ɗan wasan Jamus Miroslav Klose

Aci gaba da gasar cin kofin duniya dake gudana a ƙasar afrika ta kudu, a yau ne 'yan wasan Jamus sukayi kaca-kaca da na ƙasar Argentina daci  4 da nema. Daga cikin ƙwallayen huɗun da aka ci, uku a zura su ne a muntuna 25 bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Ɗan wasan jamus Miraslav Klose shine ya saka ƙwallaye biyu daga cikin huɗun. Wannan nasara ya baiwa Jamus sukunin tsallakewa zuwa wasan kusa dana ƙarshe, inda zata kara da wanda zata yi nasara tsakanin Spain da Paraguay .

Daga cikin wayanda suka kalli wasan na yau sun haɗa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da na Afirka ta kudu Jacob Zuma da kuma shugaban hukumar FIFA. 

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Haliba Abbas