Jamus ta sake bude ofishin jakadancinta a birnin Monrovia | Labarai | DW | 25.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta sake bude ofishin jakadancinta a birnin Monrovia

Bayan wa´adi na shekara 8 Jamus ta sake bude ofishin jakadancin ta a kasar Liberia dake Yammacin Afirka. Wannan matakin dai ya sa yanzu tarayyar Jamus ta zama ta farko a jerin kasashen KTT da ta sake bude ofishin jakadanci a birnin Monrovia. Wata sanarwa da ma´aikatar harkoin wajen Jamus a birnin Berlin ta bayar ta ce sake bude ofishin jakadancin dai na matsayin wata gudummawa da kasar ta Jamus zata bayar a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Liberia. A lokacin yakin basasan Liberia a cikin watan yunin shekarar 1997 Jamus ta rufe ofishin jakadancin ta a Monrovia.