1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nemi magance matsalolin 'yan gudun hijira

Suleiman BabayoSeptember 1, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus ta nemi ganin daukan mataki kan matsalolin 'yan gudun hijira da ake samu a nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/1GPkj
Deutschland Mariano Rajoy und Angela Merkel PK in Berlin
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kasashen kungiyar Tarayyar Turai su hada hannu domin magance matsalolin bakin haure da ake fuskanta cikin nahiyar.

Merkel ta ce 'yan gudun hijira wadanda suka tsere daga wuraren da ake yaki ya dace a raba tsakanin mambobin kasashen gwargwadon karfin kowace kasa, ta fadi haka lokacin da take ganawa da Firaminista Mariano Rajoy na kasar Spain.

Wannan yana zuwa lokacin da Firaminista Viktor Orban na kasar Hangary ya yake shirin ganawa da shugabannin kasashen Turai bisa maotsalolin kwararan bakin haure zuwa nahiyar Turai, wadanda yanzu haka suka yi kaka-gida a kasar ta Hungary, yayin da suke neman wucewa zuwa sauran kasashen na Turai masu karfin tattalin arziki.