1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta nemi a koma tattaunawar Gabas ta tsakiya

March 24, 2010

Ƙasar Jamus ta yi ƙira da lallai a koma ga shawarin gaba da gaba tsakanin Isra'ila da Palsɗinawa na gaba da gaba.

https://p.dw.com/p/Mbbn
Ministocin harkokin wajen Jamus da na Isra'ilaHoto: AP

Ƙasar Jamus ta yi ƙira da lallai a koma kan teburin shawari tsakanin Isra'ila da Palsɗinawa na gaba da gaba. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle shine ya bayyana haka yayin ganawarsa da shugabar 'yan adawan Isra'ila Tzipi Livni a Berlin. Westerwelle ya jaddada goyon bayan Jamus bisa ƙudurin da ƙasashen  da ke shiga tsakani a rikicin Gabas ta tsakiya suka zartar a birnin Moscow, wato ƙasashen Amirka da Rasha da Tarayyar Turai haɗe da Majalisar Ɗinkin Duniya. Ministan na harkokin wajen Jamus, yace kamata ya yi a haɗa da jam'iyyun adawa wajen tattaunawar. Tun da farko dai a jiya an rawaito Westerwelle yana mai cewa ci gaba da gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ke yi a yankunan larabawa, wani babban tarnaƙine kan shirin samar da ƙasashe biyu masu maƙobtaka da juna. Tzipi Livni da Guido Westerwelle sun kuma tattauna batun ƙaƙabawa Iran ƙarin takunkumin karya tattalin arziki, a dai-dai lokacin da Isra'ila ke begen ganin hakan ta faru cikin gaggawa. Minstan na harkokin wajen Jamus ya kuma yace ya yi takaicin ganin Iran taƙi bin ƙa'idojin hukumar ƙayyade yaɗuwar makamen nukiliya wato IAEA ta gitta mata.

DPA

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal