1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta naɗa sabon shugaban hukumar BND

Gwamnatin Jamus ta Tabbatar da sauke shugagan hukumar leƙem asirin ƙasar BND Gerhard Schindler tare da naɗa wani sabo watau Bruno Kahl.

Bruno Kahl Leiter der Abteilung VIII im Bundesministerium der Finanzen

Bruno Kahl SABON shugaban hukumar leƙen asiri na Jamus BND

An sauke Gerhard Schindler hekaru biyu kafin wa'adin saukarsa daga muƙamin.A cikin wata sanarwa da ma'aikatar faɗar shugabar gwamnatin ta bayyana ta ce Bruno Kahl shi ne zai maye gurbin Schindler

Masu aiko da rahotannin na cewar tsige jami'in daga hukumar leƙen asiri na Jamus ba ya rasa nasaba da satar bayyanan siri na sauraron wayar salula na shugabar gwamnatin Angela Mrkel da hukumar leƙen asiri ta Amirka ta riƙa yi tare da na wasu sauran manyan jami'an.Sabon shugabnan hukumar ta BND mista Bruno Kahl ya yi aiki a baya a ofishin ministan kuɗi na Jamus.