Jamus ta naɗa sabon shugaban hukumar BND
April 28, 2016Talla
An sauke Gerhard Schindler hekaru biyu kafin wa'adin saukarsa daga muƙamin.A cikin wata sanarwa da ma'aikatar faɗar shugabar gwamnatin ta bayyana ta ce Bruno Kahl shi ne zai maye gurbin Schindler
Masu aiko da rahotannin na cewar tsige jami'in daga hukumar leƙen asiri na Jamus ba ya rasa nasaba da satar bayyanan siri na sauraron wayar salula na shugabar gwamnatin Angela Mrkel da hukumar leƙen asiri ta Amirka ta riƙa yi tare da na wasu sauran manyan jami'an.Sabon shugabnan hukumar ta BND mista Bruno Kahl ya yi aiki a baya a ofishin ministan kuɗi na Jamus.