1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta miƙa ta'aziyar ta game da rasuwar shugaban Najeriya

May 7, 2010

Shugaban Jamus Horst Köhler yace Jamus tayi rashin abokin tafiya wajen ƙulla dangantaka tsakanin ƙasashen biyu

https://p.dw.com/p/NGs7
Shugaban Jamus Horst Köhler tare da marigayi Umaru Musa Yar'aduaHoto: picture-alliance / dpa / AP / DW Montage

Shugaban Jamus Horst Köhler yabi sahun shugananin duniya wajen miƙa saƙon ta'aziyar sa ga al'uman Najeriya bisa rasuwar shugaba Malam Umaru Musa Yar'adua. A saƙon wanda ofishin Jakadancin Jamus a Najeriya ya fitar a jiya, shugaba Köhler ya yaba da halayen ƙwarai na marigayi shugaba Yar'adua musanman na tabbatar da doka da oda da kuma zaman lafiya. Yace Jamus tayi rashin abokin tafiya wajen ƙulla dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, don haka yayi fatan 'yan Najeriya zasuyi koyi da halayen marigayin. Itama Ƙungiyar tarayyar Turai ta miƙa saƙon ta'aziyyar ta ga al'ummar Nijeriya bisa rasuwar shugaban Nijeriyan,  wanda ƙungiyar ta bayyana da cewar, ya bayar da kyakkyawar gudummuwar sa wajen tabbatar da tsarin dimoƙraɗiyya a Nijeriya, da kuma samar da zaman lafiya a ɗaukacin nahiyar Afirka baki ɗaya. Shugaban hukumar tarayyar Turai Hose Manuel Barroso, ya ce marigayi 'Yar'adua ya bar kyakkyawan misali ta fuskar shugabanci, wanda zai kasance abin koyi ga sauran shugabanni. Shi kuwa shugaban Kenya Mwai Kibaki cewa ya yi nahiyar Afirka ta rasa gwarzon shugaba wanda ya nuna halin dattaku a yadda ya gudanar da harkokin shugabancin sa a ɗaukacin rayuwar sa. Shugaban Laurent Gbagbo na ƙasar Code Vore kuwa yabawa marigayi 'yar'adua ya yi bisa irin jagorancin da ya yi a ƙungiyar kasuwar tarayyar yammacin Afirka ECOWAS .

Mawallafi: Babangida Jibril   

Edita: Halima Balaraba Abbas