Jamus ta kirkiro matattarar tara bayanai | Labarai | DW | 01.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta kirkiro matattarar tara bayanai

Yan majalisar dokokin Jamus sun amince da kudurin kirkiro wata matattarar bayanai,wacce zata taimaka wajen yaki da ayyukan yan ta´adda da kuma ta´addanci.

Dokar wacce ake sa ran fara amfani da ita a shekara mai zuwa, an bayyana cewa zata taimaka kwarai, wajen gano mutanen da ake zargi da ayyukan ta´addanci.

Ana dai sa ran wannan cibiya zata dinga tara bayanai ne dake da jibinta da suna da makamantan su, na ire iren mutanen da ake zargi da hada baki wajen shirya ko aiwatar da ayyukan ta´addanci.

Haka kuma dokar zata bawa ofishin koli na kasa mai bawa kundin tsarin mulkin kasar kariya iko, na tantance bayanai ta fannonin wayar tarho da hada hadar kudade da kuma ta jiragen sama.