Jamus ta kirkiro matakan dakile ayyukan ta´addanci | Labarai | DW | 05.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta kirkiro matakan dakile ayyukan ta´addanci

Ministocin harkokin cikin gida na tarayya da jihohi a Jamus, sun

amince da kirkiro wasu sabbin matakai, da zasu taimaka wajen dakile ayyukan ta´addanci a fadin kasar baki daya.

Ministocin dai sun cimma matakin samar da sabbin matakan ne, a lokacin wani taro da suka gudanar a birnin Berlin.

Daga cikin sabbin matakan da ministocin suka cimma, akwai bukatar samar da wani injin samar da bayanai da zai dinga taimakawa masu bincike gano mutanen da ake zargi, da kokarin gudanar da danyan aikin kai hare haren ta´addanci.

A cewar ministan kula da harkokin cikin gida na Jamus, Wolfgang Schäuble, kirkiro da wannan injin samar da bayanai abu ne daya zo a dai dai lokacin daya dace, domin a cewar sa an dade ana tunanin samar da wani abu mai kama da haka.

To sai dai kuma, da yawa daga cikin Jamusawa na jin tsoron cewa wannan mataki ka iya cin karo da wasu daga cikin yancin su.

Daukar wannan mataki dai a cewar bayanai, yazo ne makonni kadan bayan kai wasu hare haren kunar bakin wake kann wasu jiragen kasa biyu da bai samu nasara ba.