Jamus ta karrama Desmond Tutu | Labarai | DW | 03.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta karrama Desmond Tutu

Jamus ta karrama shugaban addinin kirista na ƙasar Afrika ta kudu, wato Desmond Tutu da lambar yabo mafi girma ta ƙasar. Tsohon Archbishop ɗin ya samu lambar ne, a sakamakon ayyukansa na wa´azin wanzar da zaman lafiya. Ƙaramar minista a ma´aikatar tattali da raya ƙasashe ta Jamus, Hedemarie Wieczorek-zeul ta ce lambar yabon na a matsayin alamace ta zaman lafiya da adalci a Duniya. Ministar ta kuma tabbatar da cewa Desmond Tutu, mutunne daya fita zakka a tsakanin tsaransa, dangane da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afrika ta kudu. Desmond Tutu mai shekara 76, ya taɓa karɓar kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 1984.