1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta karbi ragamar tsaron tashoshin ruwan lebanon

October 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bufu

A yau Jamus ta karɓi jagorancin sojojin ruwa na Majalisar ɗinkin duniya daga hannun Italiya waɗanda aka ɗorawa alhakin kula da kan iyakokin ruwan Lebanon bayan yakin Israila da Hizbullah. A wani biki da aka gudanar yau a babbar tashar ruwan Beirut, Kwamadan Sojin ruwan Italiya Admiral Giorgi ya miƙa ragamar gudanarwar tsaron ga kwamandan sojin Jamus Admiral Andreas Krause. Bikin ya kuma sami halartar kwamandan sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya UNIFIL. Baki ɗaya Jamus ta tura sojoji 2,400 zuwa Lebanon a karon farko da zata yi aikin kiyaye zaman lafiya a gabas ta tsakiya tun bayan yaƙin duniya na biyu. Aikin dakarun zai kasance sanya idanu domin hana fasaƙwaurin makamai da kuma taimakawa sojojin Lebanon kare kan iyakokin ruwan.