Jamus ta kame wasu ′yan IS biyar | Labarai | DW | 08.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta kame wasu 'yan IS biyar

Hukumomin shari'a a nan Jamus sun sanar da kame wasu mutane biyar da ake zargi da kafa wani gungu na 'yan Salafiya masu da'awar jihadi a cikin kasar da kuma ke yi wa Kungiyar IS rijistan sabbin mayaka a cikin kasar.

Hukumomin shari'a a nan Jamus sun sanar da kame wasu mutane biyar da ake zargi da kafa wani gungu 'yan Salafiya masu da'awar jihadi a cikin kasar da kuma ke yi wa Kungiyar IS rijistan sabbin mayaka a cikin kasar.

 

Sun bayyana cewa Jagoran gungun mutanan wadanda an kame su ne a cikin jihohin Saxony da North Rhine-Westphalia, wani dan asalin kasar Iraki ne dan shekaru 32 mai suna Ahmad Abdulaziz Abdullah da aka fi sani da lakabin Abou Walaa, sauran manbobin gungun sun hada da wani Hasan dan Turkiya dan shekaru 50, da Boban wani dan asalin kasar Jamus da Sabiya dan shekaru 36, da Mamoud wani dan kasar ta Jamus mai shekaru 27 da kuma wani dan asalin kasar Kamaru mai suna Ahmed dan shekaru 26.

 

Hukumomin shari'ar kasar ta Jamus sun ce binciken da suka gudanar ya zuwa yanzu ya nunar da cewa tuni gungun na Abdulaziz Abdullah ya yi nasarar aikawa da wani matashi da illahirin 'yan gidansu a kasar Siriya domin shiga Kungiyar IS. A wannan Talata da gobe Laraba za a gabatar da wadannan mutane biyar a gaban alkali mai bincike domin yi masu tambayoyi.