1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kalubalanci Amirka kan Kungiyar NATO

Yusuf Bala Nayaya
February 17, 2017

Merkel ta yi wannan jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus gefenta tare da Firaminista Justin Trudeau na kasar Kanada.

https://p.dw.com/p/2XmaB
Deutschland Merkel und Trudeau PK im Bundeskanzleramt in Berlin
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a ranar Juma'an nan cewa Kungiyar tsaro ta NATO na da muhimmanci da bai tsaya kan kasashen Turai kadai ba har ma da Amirka, Shugabar gwamnatin ta bayyana haka ne yayin da a gefe guda ake bude babban taron tsaro na birnin Munich a Tarayyar Jamus.

Merkel ta yi wannan jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin gefenta tare da Firaminista Justin Trudeau na kasar Kanada. Ta ce batun kawancen na NATO abu ne mai muhimmanci da ya kamata a tattauna sosai a kansa yayin taron na tsaro da ke wakana a birnin na Munich.

Shugabar gwamnatin mai aniya ta danganawa da taron na Munich na da buri na ji da ka sauran mahalarta taron kan babbar tambayar sanin makomar harkokin kasashen waje na Amirka a karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Jamus dai na da buri na kara yawan abin da take kashewa ta fiskar tsaro da kashi biyu cikin dari kamar yadda aka cimma matsaya a taron NATO na Wales a shekarar 2014.