Jamus ta jaddada ′yancin fasahar wake wake | Labarai | DW | 12.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta jaddada 'yancin fasahar wake wake

Bayan kukan Shugaban Turkiya Erdogan kan muzantashi da wani mawakin barkwancin Jamus ya yi, wannan matsala na neman sukurkuta dangantakar kasashen biyu.

Yanzu haka dai Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewar ko da yake suna da 'yancin fasahar wake-wake da rubuce-rubuce abin ya na da susa rai. Kazalika Shugaba Angela Merkel ta kara da cewar:

"Ina son na kara jaddadawa cewar kamar yadda muka fada a jiya cewar, muna da wasu ginshikan shika- shikai, ciki har da sakin layi na 5 wanda ya bayyana 'yancin fadar albakacin baki da kimiyya da kuma 'yancin fasahar wake-wake da rubuce-rubuce, ina ganin Turkiya da EU da Jamus kamata yayi su mayar da hankali wajen warware matsalolin 'yan gudun hijira."

Tun dai a watan Maris ne Jan Boehmermann mawakin barkancin Jamus ya rera wani wake da ke danganta shugaba Erdogan da cutar da tsiraru musamman Kurdawa da Kiristoci a kasar.