1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta haramta wata kungiyar musulmi

Germany/Islam

Hukumomin kasar Jamus sun haramta wata kungiyar musulmi bayanda suka kwace wasu takardu na kungiyar da sukayi zargin cewa kungiyar tana angiza musulmi su rinka kashe yahudawa da kiristoci kuma su kadddamar da harin kunar bakin wake a Iraq.

Hukumomin jihar Bavaria inda hedikwatar kungiyar take sunce ayyukan kungiyar wadda ta kunshi kabilu daban daban suna kawo barazana ga zamantakewar alummar Jamus da sauran jamaa baki da kuma tsaron kasar kanta.

Wanda a dangane da hakanne ministan cikin gida na Jamus din Guenther Beckstein ya kara da cewa ba za su amince da kungiyar da aka kafa da wata tsattsaurar manufa ba da kuma ta sabawa tsarin mulki kuma take kira ga tashin hankali karara ba.

Wannan matakin haramta kungiyar dai shine na baya bayannan a irin tsauraran matakan da hukumomin jihar ta Bavaria da sauran jihohi ke dauka akan kungiyoyin musulmi.