Jamus ta haramta taba sigari a maáikatun gwamnati | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta haramta taba sigari a maáikatun gwamnati

Majalisar gudanarwar gwamnatin tarayyar Jamus ta haramta shan taba sigari a dukkanin ofisoshin gwamnati da kuma motocin haya. Matakin ya biyo bayan sakamakon tattaunawa tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya a game da dokokin da suka shafi taba sigari. Bayan ganawa da shugabar gwamnati Angela Merkel gwamnonin jihohi goma sha shida na tarayyar Jamus sun sanar da aniyar tsara dokoki na bai ɗaya a game da taba sigari a watan Maris na sabuwar shekara.