Jamus ta gudanar da bikin sake hadewa a birnin Mainz | Labarai | DW | 03.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta gudanar da bikin sake hadewa a birnin Mainz

An yi kira da samar da dokar yin ci rani a Jamus yayin da kasar ke bikin cika shekaru 27 da sake hadewar Yammaci da Gabashi.

A karkashin tsauraran matakan tsaro an gudanar da bikin cika shekaru 27 da sake hadewar kasashen Jamus guda biyu, inda a bana birnin Mainz da ke jihar Rhineland-Palatinate ya karbi bakoncin bikin.

Shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier na daga cikin manyan baki da suka halarci biki da ya gudana a majami'ar birnin na Mainz karkashin taken "Jamus tsintsiya madaurinki daya".

A jawabin da ta yi Merkel cewa ta yi.

"Mun dauki nauyin ganin abubuwa sun inganta a kasarmu, mun san kuma akwai matsaloli masu tarin yawa da ya zama dole mu magance su. Muna da ginshikin tattalin arziki mai karfi na samar da kasa mai kamanta adalci da nuna wa juna zumunci."

Shi ma nasa bangaren shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier kira ya yi da a fayyace dokokin ba da mafaka da yin ci rani a Jamus domin kawar da abin da ya kira "katangar kyama" da aka gina sakamakon muhawara dangane da 'yan gudun hijira. Ya ce bai kamata a nuna halin ko in kula da irin wahalhalun da dan Adam ke fuskanta a wannan zamani ba.