1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gabatar da jadawalin dauke sojoji daga Turkiya

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2017

Ministar harakokin tsaro ta kasar Jamus Ursla Von der Leyen ta gabatar da jadawalin soma aikin kwashe sojojin Jamus daga barikin sojojin Incirlik ta Turkiya zuwa kasar Jodan.

https://p.dw.com/p/2esfl
Deutschland Ursula von der Leyen in der Generalfeldmarschall-Rommel-Kaserne
Hoto: picture alliance/dpa/B. Thissen

Ministar harkokin tsaro ta kasar Jamus Ursula Von der Leyen ta gabatar da jadawalin soma aikin kwashe sojojin Jamus daga barikin sojojin Incirlik ta Turkiya zuwa kasar Jodan. A cikin wata hira da ta yi da jaridar "Bild am Sonntag" ministar tsaron ta kasar Jamus ta ce aikin jigilar sojojin da kayan aikinsu zai dauki watanni uku ne daga Yuli zuwa Satumba. 

Amma har zuwa karshen wannan wata na Yuni sojojin kasar ta Jamus za su ci gaba da bayar da gudunmawarsu ga rundunar kawancen sojoji mai yaki da Kungiyar IS. Sai dai za a gaggauta dauke jiragen da ke jigilar kayan sojan zuwa kasar ta Jodan ta yadda za su yi saurin koma wa fagyen aiki. 

Sai dai ministar ta ce aikin dauke manyan jiragen yaki na Tornado da sauran kayan aikin zai dauki lokaci har zuwa watan Agusta ko Satumba mai zuwa. Gwamnatin kasar ta Jamus ta dauki matakin kwashe sojojinta daga kasar ta Turkiya ne bayan da gwamnatin Turkiyar ta haramta wa 'yan majalisar kasar ta Jamus ziyarar sojojin nasu a barikinsu ta birnin Incirlik na kasar ta Turkiya.