Jamus ta dauki sahihan matakn tabbatar da tsaro a gasar cin kofin kwallon kafa na dunyia | Labarai | DW | 31.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta dauki sahihan matakn tabbatar da tsaro a gasar cin kofin kwallon kafa na dunyia

Gwamnatin Jamus ta ce ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro a lokacin gasar cin kofin kwallon na duniya. Ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schäuble ya nunar da cewa gwamnatin tarayyar Jamus zata iya ba da tabbacin gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar na duniya a kasar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ministan ya bayyana haka ne a gun wani taron manema labarai na hadin guiwa da ya gudanar yau a birnin Berlin tare da shugaban kwamitin tsara shirye shiryen gasar, Franz Beckenbauer. An kira taron ne don bayyana matakan karshe da gwamnatin tarayya ta dauka kafin a fara wasannin a cikin ´yan kwanaki masu zuwa nan gaba.