Jamus ta damu da rikicin Georgia | Siyasa | DW | 12.08.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta damu da rikicin Georgia

´Yan siyasa a Jamus suna nuna damua game da yaƙin da ake don neman mallakar kudancin Ossetia.

default

Tankokin yaki a Ossetia

Ko da shike ana cikin hutu ne na lokacin bazara a nan Jamus, amma halin da ake ciki a yankin na Kaukasus yana ci gaba da daukar hankalin yan siyasa na kasar. Kara tsanantar yakli a wannan yanki, tsakanin Rasha da jamhuriyar Georgia ya tayar da damuwa mai tsanani a tsakanin yan siyasar na Jamus. Shugaban gwamnati, Angela Merkel daga inda take hutu ta tattauna ta wayar tarho sau da dama ada wadada rikicin na Kaukasus ya shafe su, kamar yadda kakakin gwamnati, Thomas Steg ya nunar.


Yace shugaban gwamnatin ta baiyana matukar damuwar ta a game da halin da ake ciki da kuma kara tsanantar yaki a wannan yanki.


Ko a jiya da rana sai da Merkel tayi magana da shugaban jamhuriyar Georgia, Mikheil Saakaschwili, inda ya nunar mata da nashi bangaren na halin da ake ciki. Kakakin gwmanati, Thomas Steg yake cewa:


Shugaban gwamnatin ta nuna masa a fili cewar a irin wannan hali abin da ake bukata shine tsagaita bude wuta cikin gaggawa ba tare da shimfida wasu sharudda ba, kuma wajibi ne duka bangarorin biyu su janye sojojin su zuwa wuraren da suke, kafin barkewar wannan tashin hankali, haka na kuma wajibi ne a dakatar da yaki ta sama da ta ruwa da kuma amfani da sojojin kasa, tilas ne kuma a mutunta yancin iyakokin jamhuriyar Georgia.


Tun a karshen makon jiya, shugaban gwamnati Angela Merkel da ministan harkokin waje, Frank Walter Steinmeier suka daidaita game da manuifofin su kan halin da ake ciki a yankin na Kaukasus. Yamnzu haka ana kokarin samun bayani game da makomar Jamusawa kimanin dari ukku dake zuauna a yankin da ake fama da yaki a cikin sa da yiwuwar kwashe su daga yankin. Kakakin ma'aikatar harkokin waje, Jens Plötner dake amsa tambaya a game da bangaren da Jamus take gani shine mai laifi a riicin tsakanin Rasha da Georgia yace:


Mu a ra'ayin mu, muna ganin game da wannan rikici, babu shakka akwai batun tsokanar fada daga bangarori da dama, wanda shine abin da yayi jagora ga tashin wnanan yaki.


Yanzu ba lokaci ne da ya dace a nemi dalilai ko mai laifi a wannan rikici ba, injio kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Jamus. To amma kakakin jam'iyar CDU na harkokin waje, Eckart von Klaeden ba tare da rufa-rufa ba ya shaidawa tashar DW a Berlin cewa:


Babu shakka duka bagarorin ukku dake da hannu a wnanan rikici, wato Georgia da yan tawayen Kaukasus da Rasha suna da alhakin barkewar yakin da kuma kara tsanmantar sa. To amma Rasha ita ce tafi taka muhimiyar rawa a tashin hankalin. Tun daga yan watannin baya Rasha take kara nuna shakku a game da yancin Georgia kan yankunan da take mallaka, yayin da sojojin Rasha dake kiran kansu na kiyaye zaman lafiya suka sha keta sharuddan yarjejeniyar zaman su a yankunan na Georgia. Saboda haka ne Rashan take da alhaki mai yawa na kara tsanantar yaki a wannan yanki.


Yakin dake gudana tsakanin Rasha da Georgia shine babban abin da za'a maida hankali kansa, lokacin ganawa tsakanin shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel da shugaban Rasha, Dimitri Medvedew a Sochi ranar Juma'a mai zuwa.

 • Kwanan wata 12.08.2008
 • Mawallafi Marx, Bettina (DW Berlin)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/EvSZ
 • Kwanan wata 12.08.2008
 • Mawallafi Marx, Bettina (DW Berlin)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/EvSZ