Jamus ta cirawa Mr Musharraf tuta | Labarai | DW | 28.11.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta cirawa Mr Musharraf tuta

Jamus ta yi maraba da matakin shugaba Musharraf na ajiye kakinsa na soji. Matakin a cewar ministan harkokin waje na ƙasar, Frank Walter Steimeir abune da zai sanar da kyakkyawan yanayi, na gudanar da zaɓe mai tsafta a ƙasar. Mr Staeinmeir ya kuma buƙaci Pakistan cire dokar ta ɓacin da ta ƙaƙaba a ƙasar. Yin hakan a cewar ministan zai taimaka wajen cimma burin da ƙasar ta sa a gaba na komawa tafarki na mulkin Dimokruɗiyya. A ranar 8 ga watan Disambar shekara ta 2008 ne aka shirya yin zaɓen gama garin a Pakistan ɗin.

 • Kwanan wata 28.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CUD4
 • Kwanan wata 28.11.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CUD4