Jamus ta ce Iran ba ta ba da amsa mai gamsarwa ga tayin ba ta taimako ba | Labarai | DW | 25.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta ce Iran ba ta ba da amsa mai gamsarwa ga tayin ba ta taimako ba

Gwamnatin tarayyar Jamus ta bi sahun Amirka da Faransa wajen nuna rashin gamsuwa da amsar da Iran ta bayar game da ba ta taimakon tattalin arziki idan ta dakatar da shirin ta na nukiliya. A lokacin da take tofa albarkacin bakin ta dangane da martanin da gwamnati a Teheran ta mayar, SGJ Angela Merkel ta ce hukumomin Iran ba su yi magana game da dakatar da aikin sarrafa sinadarin uranium ba. Merkel ta ce kin ambato wannan batu ya sabawa kiran da kasashen duniya suka yi mata na dakatar da shirinta na nukiliya da ake takaddama kai. Jamus na cikin jerin manyan kasashen duniya 6 da suka yiwa Iran tayin ba ta taimako. Kwamitin sulhu na MDD ya bawa gwamnatin Teheran wa´adin zuwa 31 ga watannan na agusta da dakatar da shirin sarrafa uranium ko kuma ta fuskanci barazanar kakaba mata takunkumi.