1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci warware takaddamar nukiliyar Iran cikin ruwan sanyi

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bukaci kasashen yamma dasu bi hanyar diplomasiyya daki daki, wajen warware rikicin nukiliyar kasar Iran.

Angela Merkel, wacce ta fadi hakan jim kadan bayan tattaunawar ta da shugaba Jacque Chirac na faransa, ta kara da cewa tana fatan duk abin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yanke a kann wannan takaddama, kasashen na yamma zasu amince ba tare da kace nace ba.

A dai ranar 2 ga watan fabarairun wannan shekara ne ake sa ran gwamnonijn hukumar ta IAEA zasu gudanar da taron nasu don nemo bakin zaren warware wannan takaddama.