Jamus ta bukaci kyautata wa rayuwar ′yan gudun hijirar Kasar | Labarai | DW | 07.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci kyautata wa rayuwar 'yan gudun hijirar Kasar

Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck ya jaddda cewar dole ne Jamus ta yi kokarin kyautata rayuwar 'yan gudun hijirar da suka shigo kasar cikin hanzari domin kaucewa matsalolin siyasa da halayyar ayyukan ta’addanci.

Shugaba Joachim Gauck ya kuma bayyana cewar irin yadda wasu abubuwa suka faru a wasu kasashe sakamakon kwararrar 'yan gudun hijirar da suke shigowa tare da muradin zama a kasashen turai, ya zama wajibi su sami horon harshen Jamusanci gami da neman aiki cikin hanzari da hakan zai yi wa kowa dadi.

Tarayyar Jamus dai na daya daga cikin kasashen Turai ta karbi bakuncin ‘yan gudun hijira sama da miliyan daya fiye da kowacce a inda yawancin su suka futo daga kasashen Afganistan da Iraki da Syriya.