Jamus ta bukaci a bullo da hanyoyin sanar da balaoi kamr tsunami a Turai | Labarai | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci a bullo da hanyoyin sanar da balaoi kamr tsunami a Turai

Gwamnatin kasar Jamus tayi kira da a kirkiro da hanyar baiyana bullar ambaliya irin ta tsunami cikin gaugawa a bikin iyakokin ruwa na Turai dake bakin tekunan Mediterranean da Atlantika.

Ministan kula da harkokin bincike Anette Schavan ta zata mika wannan shawara ga takwarorinta wajen taronsu na kasa da kasa da zaayi nan gaba.

Tace dole ne nahiyar turai ta kasance cikin shirin kot a kwana domin magance balaoi kamar na tsunami data abkawa nahiyar Asiya a bara.