1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bawa Lebanon tallafin Euro million guda

Gwamnatin Jamus ta sanar da bada tallafin kudade euro million guda wa alummar fararen hula da suka jikkata a sakamakon hare haren izraela a kasar Lebanon.Ministan harkokin waje na Frank-Walter Steinmeier, wanda ya sanar da hakan a yau ya kuma bayyana cewa ya zuwa jiya an cimma kwaso jamusawa 750 daga Beirut,ayayinda ya zuwa yau kimanin 1,000 zasu iso.

Hakazalika Daruruwan Amurkawa dake Lebanon ake jibgawa a jiragen ruwa,akokarinsu na gujewa wannan kasa dake cigaba da fuskantar lugudan wuta da hare haren boma boman Izraela.Anasaran jirgin ruwan zai kwashi kamar Amurkawa 1,000 zuwa Cyprus.Ayayinda jiragen saman Amurkan ke cigaba da gaggauta deban maaikatanta daga ofishin jakadancin kasar dake arewacin Beirut.