Jamus ta bada shawara kan inganta simadarin uraniyum | Labarai | DW | 17.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bada shawara kan inganta simadarin uraniyum

Kasar Jamus ta shawarta hada hannu wajen inganta uranyium ga kasashe tare da sa ido na MDD,a maimakon barin kasashe samarda nasu fasahohi,domin kare abinda ta kira kera bamabamai.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmiere ya fadawa wata jarida anan Jamus cewa,hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa zata iya kula da wadannan kayaiyaki.

Steinmeire ya kuma jaddada cewa,diplomasiya itace kadai hanya da zata magance rikicin nukiliya na Iran.