Jamus ta amince da rage hayakin masana`antunta | Labarai | DW | 06.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta amince da rage hayakin masana`antunta

Gwamnatin Jamus ta amince kan wani shiri na bilioyin euro na rage hayaƙin masana`antunta. Nan zuwa shekara ta 2020 gwamnatin ta ce zata rage kusan kashi 40 cikin dari .Shirin ya haɗa da inganta hanyoyin samarda makamashi,tare da faɗaɗa harkokin sabunta makamashin da sabon tsari na gine gine da ba zasu bukaci makamashi mai yawa ba. Jamus ita ce kasa dake kan gaba wajen yada hayaki mai guba a turai inda take fitar da kashi uku bisa ɗari na dukan hayaki dake gurɓata muhalli.