1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta amince da hadewar iyalan 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
February 2, 2018

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da batun sake hadewar iyalan 'yan gudun hijira da suka shigo kasar. Iyalai 1000 a wata za su samu damar shigowa Jamus domin sake hadewa da danginsu.

https://p.dw.com/p/2s1w4
Deutschland Fest des Fastenbrechens Zuckerfest
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

Sai dai a hannu guda jam'iyyun masu ra'ayin 'yan mazan jiya ba su so wannan matakin ba, a ganinsu kamata ya yi a dakatar da batun na sake hadewar iyalan 'yan gudun hijira har sai an samu amincewa ta bai daya. Wannan dokar ita ce ta farko da kokarin kafa gwamnatin hadakar bai kammala cimma matsaya a kanta ba.

Katrin Göring-Eckardt
Shugabar jam'iyyar the Green, Katrin Göring-EckhardtHoto: picture-alliance/ZB

A karshen watan Janairu ne dokar hana sake haduwar iyalan na 'yan gudun hijira ke karewa, ya zama tilas majalisar dokokin ta Bundestag ta yanke hukunci nan kusa, ta kuma yanke hukunci ta hanyar kada kuri'a daga wakilan jam'iyyun CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da abokiyar tagawaitakarta ta CSU sai kuma jam'iyyar SPD da take tattauna batun yiwuwar shigarta gwamnati a kokarin da ake na kafa gwamnatin hadaka a Jamus. Sun amince da batun sake hadewar iyalan, sai dai an kayyade su zuwa 1000 a kowane wata kamar yadda Katrin Göring-Eckhardt shugabar jam'iyyar adawa ta jam'iyyar the Green mai kare muhalli ke cewa.

"Ana so a soke batun bayar da damar sake hadewar iyalan ne baki daya, ba a martaba dokokin kasa da kasa, sai dai an yi afuwa ga wasu adadin mutane da ya kasance tamkar an zabo su ne."

A na iya cewa dai tamkar an soke 'yar guntuwar damar da 'yan gudun hijirar ke da ita, hakan zai shafi da dama daga cikin 'yan gudun hijirar da ke zaune a Jamus. An kayyade wasu adadi ne kawai a wata, inda jam'iyyun da ke son kafa gwamnatin hadaka suka amince ba tare da tunani ba na adadin 'yan gudun hijirar da za su shigo Jamus duk shekara su 180.000 zuwa 220.000. A ta bakin Stephan Mayer.

Deutschland Bundestag- Stephan Mayer
Dan majlisar dokokin Jamus, Stephan MayerHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

"A bayyane yake cewa batun sake hadewar iyalan zai taimaka wa wasu kamar yadda muka amince a sabon tsare tare da jam'iyyar SPD kan shigowar iyalai daga 180,000 zuwa 200,000  shekara. Daga ranar daya ga watan Agusta mai zuwa zamu fara bayar da damar hadewar ta hanyar shigowar akalla iyalai 1,000 duk wata. Iyalan da suka tsinci kansu cikin halin kunci na rashin lafiya da halin tsaka mai wuya sakamakon yaki, su ne za a bai wa damar shigowa Jamus." 

A yanzu da hadakar 'yan majalisar suka shiga tattaunawa kan batun 'yan gudun hijirar da taimakon jam'iyyun da ke mulki, koda hakan ya janyo kin amincewa daga bangarori da dama, batun kayyade adadin wadanda za su shigo din ka iya janyo abin da aka jima babu a Jamus, wato doka ta daban a kan 'yan gudun hijira.

Deutschland Berlin - Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a zauren majalisaHoto: Getty Images/S. Gallup

Kasashe kamar Kanada na da dokoki masu sauki kan 'yan gudun hijira. Adadin ka iya nuna yawan mutanen da aka amince su shigo cikin kasa da kuma daga kasashen da aka amince su shigo da ka'idojin da ya kamata su cika.

Ana tattauna batun adadin da kuma ka'idojin duk shekara a majalisa, abin da ke faruwa ke nan yanzu a Jamus. A yanzu dai batun ya shafi 'yan gudun hijira ne kawai, amma wa ya sani ko a nan gaba jam'iyyun da ke mulki da hadin gwiwar SPD za su samar da irin wannan doka ga iyalan da suke zuwa Jamus domin yin aiki, ta yadda tuni za a fara lissafi, misali yawan ma'aiktan jinyar da ya kamata su shigo Jamus.