Jamus: Rabuwa Da Sake Haɗewa | Samun Haɗin Kan Jamus | DW | 16.03.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Samun Haɗin Kan Jamus

Jamus: Rabuwa Da Sake Haɗewa

Juyin juya hali a cikin lumana, rushewar katanga, haɗin kan Jamus: Wannan maƙala ta musamman „Jamus: Rabuwa da sake haɗewa“ na nuna turbar da aka ɗauka zuwa haɗin kan Jamus- wadda kuma aka ci gaba da bi.

A shekara ta 2009 rushewar katangar Berlin ta kai shekara 20, a shekara ta 2010 za a yi bikin tunawa da haɗin kan Jamus a yankunan gabas da na yamma a cikin ƙasar. DW-WORD.DE na tunatarwa a kan manyan-manyan al'amuran tarihi da suka auku tsakanin ƙasashen Jamusawa biyu, haka kuma da suka shafi Jamusawa gaba ɗayansu: muna siffanta gwarzaye waɗanda suka yi wannan juyin juya hali a cikin lumana a Jamus Ta Gabas, muna ba su damar shaidawa kuma muna zayyana muku labarun waɗanda suka ci nasara da kuma waɗanda suka sha kaye a kan turbar haɗin kan Jamus.