1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Puigdemont ya fice daga gidan kaso

Yusuf Bala Nayaya
April 6, 2018

Kasar Spain ta bayyana cewa za ta mutunta matsayar da kotu a Jamus ta cimma a dangane da bukatar tiso keyar tsohon jagoran yankin Kataloniya Carles Puigdemont daga Jamus zuwa kasar.

https://p.dw.com/p/2vbMc
Carles Puigdemont
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Mayo

Wata kotu a Jamus ta bayyana a ranar Alhamis cewa ta yi fatali da bukatar a mayar da tsohon jagoran yankin na Katalioniya zuwa Spain bisa laifi na yi wa mahukunta tawaye a lokacin kamfe na neman yankinsa ya samu 'yancin gashin kai daga Spain sai dai kotun ta ce za ta iya duba bukatar mahukuntan na mayar da shi gidan bisa wasu laifukan da ke zama kanana kamar almubazzaranci da kudaden al'umma. Puigdemont ya fice daga gidan kaso da ake tsare da shi a Jamus bayan cika wasu sharuda da suka sanya aka sake shi.

Tuni mahukuntan Spain suka ce za su mutunta hukuncin da kotun Jamus ta yanke. Mai magana da yawun gwamnati a Spain Inigo Mendez de Vigo ne ya bayyana haka a wannan rana ta Juma'a wajen taron manema labarai da ya saba yi a duk mako.