1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son a kasafta 'yan gudun hijira

Yusuf Bala/ASSeptember 15, 2015

Jamus ta bukaci a matsa lamba ga kasahen Turai don su amince da raba daidai na 'yan gudun hijirar da ke shiga Turai wanda galibinsu yanzu haka ke shiga kasar.

https://p.dw.com/p/1GWwl
Mazedonien Griechenland Flüchtlinge bei Gevgelija
Hoto: picture-alliance/epa/G. Licovski

Ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maizière ya bayyana bukatar da ke akwai na matsawa kasashen da ke gabashin Turai lamba kan karbar wani kaso daga cikin 'yan gudun hijirar da ke cigaba da kwarara Turai. Wannan kiran da ministan na harkokin cikin gidan Jamus din ya yi dai ya biyo bayan bijirewar da kasashen suka yi na karbar bakin duk kuwa da cin moriyar da na tallafin da suke karba daga hannun kungiyar EU kan wannan batu.

To sai da ministan harakokin wajen kasar Luxemburg Jean Asselborn ya shaida wa manema labarai cewa akasarin kasashen Turai 28 sun amince a bisa manufa ta kashin kansu su bai wa bakin hauren mafaka a kasashensu sai dai sun nunar da cewa a halin yanzu ba su kintsa ba, abin da ya sa ministan harkokin cikin gidan Jamus ya ce batun cewa ma ba a kintsa ba a yanzu ba shi ne mafita ba duba da irin matakin da Girka ke son dauka.

Symbolbild - Flüchtlinge
Wasu kasashen Turai sun ce suna shiri na karbar kasonsu na 'yan gudun hijrara da suka shiga Turai.Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Giannakouris

Shugabanni daga kungiyar ta EU dai sun amince cewa akwai bukatar sake zama na ministocin harkokin cikin gidan kasashen daga wannan kungiya mai mambobi daga kasashe 28 kuma sun ce suna son ganin an yi taron ne ranar takwas ga watan Oktoba inda za a ga yadda za a rarraba wadannan 'yan gudun hijira kimanin 120,000 tsakanin kasashen na EU.

Symbolbild Ungarn Grenze Zaun
Hungary ta sanya shingen waya mai reza da zai hana 'yan gudun hijira shigar mata kasa.Hoto: picture alliance/CITYPRESS 24/Hay

Kasashen da suka rigaya suka yi kememe wajen amincewa da batun karbar 'yan gudu hijirar dai sun hada da Girka da Italiya da Hungary wacce yanzu haka ta rufe kan iyakarta da kasar Sabiya kuma ta sanya shinge da nufin hana 'yan gudun hijira da sauran bakin hare shiga kasarta. Tuni ma dai wadannan matakai da ta dauka suka fara yin tasiri kan masu son shiga Turai din ta kasar, lamarin da ke cigaba da shan suka daga kasashen duniya.