1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na shirin aikewa da sojin ta izuwa Libanon

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buit

A nan gaba a yau ake sa ran karamar majalisar dokokin Jamus zata kada kuri´ar amincewa da tura dakarun sojin ta izuwa Libanon.

Bataliyar sojin na Jamus dai ana sa ran zata gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya ne a Libanon din ne karkashin laimar Mdd.

Ya zuwa yanzu dai tuni shugabar gwamnatin kasar, wato Angela Merkel ta bayyana wannan yunkuri da cewa abin tarihi ne ga kasar.

To sai dai wannan kalamin nata yazo ne a dai dai lokacin da da yawa daga cikin Jamusawa ke adawa da wannan shiri.

kafafen yada labaru dai sun rawaito, Ulrike Merten, daya daga cikin mamba a kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar daga jam´iyyar SPD, na cewa, akwai bukatar yin taka tsa tsan ako da yaushe wajen daukar mataki irin wannan dake cike da hatsari, ga soji maza da mata.

A dai karkashin wannan tsari , ana sa ran Jamus zata aike ne da dakarun soji dubu biyu da dari 4 don gudanar da wannan gagarumin aikin.