1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na neman sabuwar hulda da Rasha

Koschyk, Maximiliane AH
March 17, 2018

A yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Rasha, halin da ake ci na zaman doya da man ja tsakanin Rasha da kasashen Turai ya sa manazarta na hasashen cewar akwai bukatar Jamus ta sake fasalin huldarta da Rasha.

https://p.dw.com/p/2uX0M
Russland | Pressekonferenz Merkel Putin
Hoto: Getty Images/AFP/A. Nemenov

Vladmir Putin ya kan tsokana, amma kuma Angela Merkel ta kan yin juriya. A cikin wata hira da shugaban na Rasha ya yi da wata jaridar kwanaki kadan kafin zaben, ya shaida cewar shugabar gwamatin ta Jamus ta kan aike masa da barasa Radeberger Pils. Barasar da ake yi a Jamus wace ya saba sha tun lokacin Jamus ta Gabas. Ko da shi ke Angela Merkel ta tabbatar da hakan amma dai furcin na Vladmir Putin bai yi mata dadi ba. Sannin ko wane dai a yanzu dangantaka tsakanin Jamus da Rasha ba ta tafiya da kyau. Barazanar da Jamus ta yi wa Rashar a kwanan nan bayan sanarwar da ta bayyana a farkon shekara na kaddamar da wani sabon shirin na makamai masu linzame, bai tada hankalin Vladmir Putin ba. Kuma Stefan Meister kwararre a kan kasar Rashar na cibiyar nazarin siyasar kasashen waje ya ce da wuya, ko nan gaba huldar tsakanin Jamus da Rasha ta daidaita. 

Russland | Merkel trifft Putin
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Kochetkov

Rashar na yin amfanin da yakin da take da wasu kasashen duniya domin tilasta bukatunta ga kasashen Turai. Tsarin da wasu Jamusawa ke ganin rashin tabbas ne na kasar misali batun ba da guba ga wani tsohon jami'in leken asirin na Rasha a Birtaniya wanda Birtaniya ke zargin Rasha da laifin aikatawa. Da kuma batun fashi ta hanyar intanet wanda masu yin kutse na Hackers na Rasha suka yi a kan majalisar Bundestag da wasu ofisoshin ministocin na Jamus, ya sa fargaba a zukatun al'ummar Jamus a game da rashin cikakken tsaro. Gustave Gressel kwararre a kan sha'anin tsaro na majalisar hulda ta kasa da kasa na kungiyar tarrayar Turai ya ce Jamus da Faransa yakamata su dage wajen neman abin da ba zai zama ila ga Turai baki daya ba daga Rasha, kana ya ce dole Jamus ta nemi yin sabuwar hulda da Rasha.