1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na neman kwato wa 'yan Yazidi hakki

Mouhamadou Awal Balarabe
January 19, 2023

'Yan majalisar dokokin Jamus sun amince da kashe-kashen da kungiyar IS ta yi wa 'yan kabilar Yazida a Iraki a matsayin kisan kare dangi, tare da yin alkawarin taimaka wa 'yan tsirarun da ke magana da harshen Kurdawa.

https://p.dw.com/p/4MSIK
Lokacin da ake muhawarar kare 'yan Yazidi a majalisar dokokin JamusHoto: Carsten Koall/dpa/picture alliance

Daukacin 'yan majalisa da suka halarci zaman a Berlin ne sun kada kuri'ar amincewa da wannan doka, sakamakon azabtarwa da kisa da wulakanci da 'yan kabilar Yazidi 5,000 suka fuskanta daga mayakan IS masu kishin Islama a shekara 2014.

 Ita dai Jamus ta ksance kasar yammacin duniya ta hudu da ta dauki nauyin kare 'yan kabilar Yazidi baya ga Beljiyam da da Ostareliya da suka aiwatar da irin wannan mataki. Tuni ma Nadia Murad da ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2018, wacce ita ma Yazidi ce ta yaba da yadda Jamus ta nuna misali da kuma kira ga dukkan gwamnatocin da su amince da kisan kiyashin Yazidi a hukumance.