Jamus na fargabar leken asirin Rasha a zaben majalisa | Labarai | DW | 08.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na fargabar leken asirin Rasha a zaben majalisa

Shugabar Gwamnati Angela Merkel ta ce tana fargabar yiwuwar kasar Rasha ta nemi ta yi katsalandan cikin harakokin zaben 'yan majalisar dokoki da kasar za ta shirya a shekara ta 2017 da nufin haddasa rudani.

A daidai lokacin da ake gudanar da zabuka a kasar ta Amirka, a nan Jamus Shugabar Gwamnatin Angela Merkel ta ce tana fargabar yiwuwar kasar Rasha ta nemi ta yi katsalandan cikin harakokin zaben 'yan majalisar dokoki da kasar za ta shirya a shekara ta 2017.

 

Merkel wacce ta bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ta gudanar a wannan talata a birnin Berlin tare da takwararta ta kasar Norway Erna Solberg ta ce akwai yiwuwar kasar ta Rasha ta nemi satar bayanai ta kafar sadarwar zamani ta intanet da wallafasu ko kuma yada labaran karya da nufin kawo rudani a cikin zaben.

 

Merkel ta ci gaba da cewa doli su dauki matakai na rigakafi, domin matsalar na iya bayyana tun a lokacin yakin neman zabe, wannan kuwa domin kaucewa fadawa yadda ta kasance ga 'yar takarar neman shugabancin Amirka a karkashin inwar Democrates Hillary Clinton. Dama dai hukumar leken asirin kasar ta Jamus ta zargi a wannan shekara kasar ta Rasha da aiwatar da leken asiri kan wasu jam'iyyun siyasa dama wasu manyan hukumomin gwamnatin kasar.