Jamus na bikin hadewar ta a matsayin kasa guda | Labarai | DW | 03.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na bikin hadewar ta a matsayin kasa guda

A Jamus a yaune ake gudanar da bukukuwan tunawa da ranar hadewar Jamus ta gabas da kuma ta yamma a matsayin dunkulalliyar kasa guda.

A lokacin da take jawabin bude bikin da ake gudanarwa a birnin Kiel, shugabar gwamnati Angela Merkel, tayi tsokaci ne a game da muhimmancin dake tattare da samun yanci ne.

Bugu da kari Angela Merkel, ta kuma nuna farin cikin ta a game da wannan rana da cewa rana ce dake kunshe da tarihi a cikin ta.

Shima dai shugaban kasa Horst Köhler bayyana farin cikin sa yayi a game da ranar.

Rahotanni dai sun rawaito ministar raya kasashe na cewa babu ja an samu ci gaban a jihohin dake gabashin kasar, to amma har yanzu zasu ci gaba da kasancewane karkashin tallafin jihohin dake yammaci a kalla shekaru 15 ko kuma 20 masu zuwa.