1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar shugaban gwamnati ta sha kaye

Binta Aliyu Zurmi
May 15, 2022

Jam'iyya mai mulki a Jamus ta SPD ta sami mumunan koma baya a zaben jihar 'yan majlisa a North Rhine-Westphalia, jihar da ta fi yawan al'umma a kasar.

https://p.dw.com/p/4BL26
Deutschland | Landtagswahl NRW | Hendrik Wüst
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

Sakamakon farko na kuri'un da aka kada a zaben 'yan majlisun jihar North Rhine-Westphalia da ke Jamus, na nuni da cewar jam'iyyar shugaban gwamnati Olaf Scholz ta sami mumunan koma baya a wannan zaben da ke zama zakaran gwajin dafi ga sabuwar gwamnatin da ta dare karagar mulki a shekarar da ta gabata.

Jam'iyyar CDU wacce ta yi nasara a zaben ta sami kaso 35 cikin dari. Ita kuwa jam'iyya mai mulki ta SPD ta sami kaso 28 ne kacal cikin dari, inda ta yi kasa da sama da kaso 3 a zaben na jihohi da ya gudana.

Da wannan sakamako hakan na nuni da cewar gamayyar kawancen gwamnati da ke tsakanin jam'iyyun CDU da FDP, yanzu haka ba za su sami rinjaye a majalisar ba abin da ke nuni da cewa tilas a sake zama kan teburin tattauna yiwuwar sake kafa gwamnatin hadaka a jihar.