Jamus da Tunisiya za su yaki ta′addanci tare | Siyasa | DW | 15.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus da Tunisiya za su yaki ta'addanci tare

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Tunisiya Yousseh Chahed sun tattauna kan hanyoyin yaki da ta'addanci, bayan da dimbin 'yan Tunisiya suka kai hare-haren ta'addanci.

Wannan ziyara ta zo lokacin da hukumomin Jamus ke neman hanyoyin harzarta mayar da 'yan Tunisiya gida wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka, tun bayan harin da wani dan kasar ya kai birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.  Anasa bangaren Firaminista Yousseh Chahed na Tunisiya ya jaddada muhimmanci aiki tare domin dakile ta'addanci.

Sunan kasar Tunisiya ya kara fitowa bayan harin da Anis Amri ya kai birnin Berlin na Jamus, abin da ya halaka mutane 12, kana wasu da dama suka samu raunika, sannan aka sake kama wani dan kasar bisa zargin kitsa ta'addanci. Ridha Raddaoui wani lauya a kasar ta Tunisiya ya gudanar da bincke kan yadda kasar ke sahun gaba wajen samar da 'yan ta'adda da sansanonin horas da su, inda kashi 70 cikin 100 na 'yan ta'adda suka samu horo. 

Ya ce "Fiye da kashi 3 cikin hudu na 'yan kasa da shekaru 34 ne. Wadannan matasa ne masu jini a jika, wadanda sun kasance ba su karkashin matsin lamba na kama karya ba, kuma galibi suna da ilimi, inda kashi 40 cikin 100 suka halarci jami'a."

 

Rashin aiki ga matasa yana kara kaimin jefasu cikin kungiyoyin 'yan ta'adda, kuma a cewar Heba Morayef shugabar kungiyar ofishin kungiyar Amnesty da ke arewacin Afirka, mahukuntan kasar ta Tunisiya sun gaza bullo da wata hanya ta yaki da ta'addaci mai inganci tun bayan juyin juya halin da ya kawo karshen gwamnatin kama karya da Zine Abidine Ben Ali shekaru 6 da suka gabata.

 

Sauti da bidiyo akan labarin