1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da rikicin Gabas Ta Tsakiya

YAHAYA AHMEDJuly 18, 2006

Jamus na cikin ƙasashen ketaren da a halin yanzu ke kwashe 'yan ƙasarsu daga Lebanon, saboda hare-haren da Isra'ila ke kai wa wannan ƙasar. Tun da Ƙungiyar Hizbullahi ta cafke wasu sojojin Isra'ila guda biyu ne, Isra'ilan ta fara kai hare-haren mai da martani kan ƙasar Lebanon. A halin yanzu dai, farkon tawagar Jamusawan da aka kwaso daga Lebanon, ta sauka a birnin Düsseldorf yau da safen nan.

https://p.dw.com/p/Btz4
Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier
Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter SteinmeierHoto: PA/dpa

Jamus na cikin ƙasashen da suka fara kwaso ’yan ƙasarsu daga Lebanon, sakamakon hare-haren bamabaman da jiragen saman yaƙin Isra’ila ke ta kaiwa a biranen ƙasar, a wani sabon mataki na rikicin da ya ɓarke a yankin na Gabas Ta Tsakiya. Yayin da Isra’ila ke ta jefa bamabamai a Lebanon ɗin, ita kuma ƙungiyar Hizbullahi, wadda cafke sojojin Isra’ila da ta yi a kudancin Lebanon ne ya janyo ɓarkewar wannan rikicin, tana ta ƙara harba rokoki zuwa biranen Isra’’ila kamarsu Haifa.

Al’amura dai sai ƙara taɓarɓarewa suke yi a yankin, musamman a ƙasar Lebanon, inda a ko wace rana sai an sami ƙarin yawan fararen hula da ke rasa rayukansu, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa don mai da martani ga rokokin da ƙungiyar Hizbulllahi ke ta harba mata.

A birnin Beirut dai a halin yanzu, ofishin jakadancin ƙasashen ƙetare, musamman na yamma na ta hidimomin kwashe ’yan ƙasashensu ne daga birnin zuwa ƙasar Siriya a cikin bas-bas, inda daga birnin Damascus ne kuma ake kwaso su da jiragen sama. Ana hakan ne kuwa, saboda lalata filin jirgin saman Beirut da jiragen saman Isra’ilan suka yi da bamabamai.

A yau da safen nan ne farkon jirgin saman Airbus, ɗauke da fasinjoji kusan ɗari 3 dukkansu Jamusawa, ya sauko a birnin Düsseldorf. Jirgin dai ya taso ne daga birnin Damascus na ƙasar Siriya, inda aka fara kai Jamusawan da aka kwason daga Beirut a cikin motoci. Wata mace da ke cikin fasinjojin ta bayyana wa manmeman labarai irin abin ya auku gaban idanunta ne a birnin Beirut kamar haka:-

„A gabana kusan mita ɗari da inda nake ne, wata roka ta faɗo. Nan take naga baƙin hayaƙi ya tashi. Ɗana na zaune kusa da ni cikin mota. A wannan lokacin na ji tsoron mutuwa.“

A cikin sa’o’i 24 masu zuwa dai, ofishin jakadancin Jamus a birnin Beirut ya ce za a kwashe wata tawagar Jamusawan kuma zuwa birnin Damascus, inda daga nan, za su taso cikin jiragen sama zuwa gida.

A huskar diplomasiyya kuma, Jamus ta ce tana duk iyakacin ƙoƙarinta wajen ganin cewa an kwantad da ƙurar rikici a yankin na Gabas Ta Tsakiya. A cikin wata fira da ya yi da gidan talabijin nan ZDF na nan Jamus, ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier, ya bayyana cewa, harba rokoki zuwa Isra’ila da cafke sojojinta da aka yi ne ummal aba’isin wannan rikicin, wanda ke ci gaba da ta’azzara. Duk da cewa dai Isra’ilan na da ’yancin ɗaukan matakan kare kanta, Ƙungiyar Haɗin Kan Turai na yi mata kira da ta nuna sasssauci ga yadda take kai hare-harenta, don ka da a yi ta ƙara samun asaran rayukan fararen hula, inji ministan:-

„Muna kira ga Isra’ilan da ta rage tsannanin hare-harenta, don kare rayukan fararen hula, kuma don ka da ta janyo wargajjewar ƙasar Lebanon.“

Game da tambayar ko nahiyar Turai za ta ba da taimakon dakarun kare zaman lafiya ga rundunar da ake sa ran Majalisar Ɗinkkin Duniya za ta tura zuwa yankin, ministan ya bayyana cewa:-

„Har ila yau dai, ba a tsai da shawarar yin haka ba. Akwai dai ra’ayoyin da aka gabatar. Idan muka ga cewa, wannan shawarar na da ma’ana, to babu shakka Ƙungiyar Haɗin Kan Turai ba za ta juya mata baya ba.“

A birnin Berlin kuma, dubban ’yan ƙasar Lebanon ɗin mazauna nan Jamus sun yi zanga-zanga jiya ta nuna ɓacin ransu ga matakan da Isra’ila ke ɗauka na kai wa ƙasarsu hare-hare. Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun yi ta kiraye-kirayen „Allah wadai ga Isra’ila“ Rahotanni sun ce a cikin jama’an akwai kuma waɗanda suka cira hoton shugaban ƙungiyar Hizbullahi, Hassan Nasrallah, a sama, gaban ƙofar nan ta Brandenburg da ke tsakiyar birnin Berlin. Wani kakakin masu shirya zanga-zangar ya ce nan gaba ma za su ci gaba da shirya wasu jerukan gwanon.