Jamus da Rasha zaua baiwa juna cikakken hadin kai a fannoni da dama | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Rasha zaua baiwa juna cikakken hadin kai a fannoni da dama

Kasashen Jamus da Rasha sun cimma yarjejeniyar karfafa ba juna hadin kai a fannin tattalin arziki. A karshen tattaunawar yini biyu da gwamnatocin kasashen biyu suka yi a birnin Tomsk dake jihar Siberia, SGJ Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir Putin sun jagoranci bukin sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama. Kamfanin samar da iskar gas na Rasha wato Gazprom da kamfanin BASF na nan Jamus sun cimma yarjejeniyar gudanar da aikin hadin guiwa na samar da gas a yankin yammacin Siberia. A lokacin da yake magana bayan taron da suka yi shugaba Putin ya ce sun tattauna akan batutuwa da dama wadanda suka shafi matsayin kasashen biyu. Ita ma Angela Merkel ta nuna gamsuwa ga tattaunawa.