1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deutschland Menschenhandel

July 14, 2009

Wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adma a Jamus sun yunƙuro wajen ƙwatowa baƙin da ake ci da guminsu haƙƙinsu.

https://p.dw.com/p/IpL4
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP

A duk lokacin da aka yi maganar bauta ko aikin ƙwadago na dole abin da ke zuwa zukatan ɗaukacin Jamusawa shi ne lokacin mulkin ´yan Nazi ko zamanin cinikin bayi. To amma har yau ana bautar da mutane ko sa su aikin dole a ƙasashe da dama ciki har da a nan Jamus. Ire iren wannan ta´asar ba sa fitowa fili, sannan da wuya ake gano waɗanda ake ci da guminsu domin ba su da takardun izinin zama a nan Jamus. Amma yanzu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun yunƙuro don taimakawa waɗannan mutane samun haƙƙinsu.

Ɗaukacin waɗannan mutane dai suna aiki ne a gidajen sayar da abinci ko a gidajen mutane ko kuma a matsayin karuwai. Ba wanda ya san yawansu kuma saboda rashin takardun izinin zama a nan Jamus suna jin tsoron ka da a koma da su ƙasashensu na asali. Ba kuma wanda zai iya cewa ko ƙwadagon tilas ko fataucin ´yan Adama jefi-jefi ne ake yin sa a nan Jamus ko kuma ya zama ruwan dare a cikin ƙasar. To sai dai ko shakka babu da akwai wani sabon salo na bauta, kamar yadda wani bincike na ofishin ´yan sandan tarayya ya nunar. Alal misali a shekara ta 2007 mutane kimanin 700 aka gano cewa ana ci da guminsu.

Taimakawa irin waɗannan mutane shi ne burin aikin cibiyar kare haƙƙin bil Adama ta Jamus da wata gidauniyar kula da waɗannan mutane kamar yadda shugaban wannan gidauniya Martin Salm ya nunar.

Ya ce: "Saƙo ga waɗannan mutanen shi ne suna da ´yanci kuma akwai damar taimakawa musu. Saƙo ga jama´a shi ne sun san cewa ana sa mutane aikin dole a nan Jamus kuma ba za mu jurewa duk wani salon aikin dole ko bauta ba. Kuma saƙo ga masu aikata wannan laifi shi ne ana iya hukunta su kuma hukunci mai tsanani."

Wannan shirin da zai ci kuɗi euro dubu 600 tsawon shekaru uku ba wanda ke sanya dogon burin cewa zai samu nasarar da ake sa rai, musamman wajen kakkafa wuraren ba da shawarwari da zaƙulo masu aikata wannan laifi don a hukunta su. Yadda kotunan Jamus ke gudanar da aikinsu ya isa shaida ga shakkun da ake nunawa. Daraktan cibiyar kare haƙƙin bil Adama na Jamus Heiner Bielefeld ya yi ƙorafin yana mai cewa bayan kotu ta saurari waɗanda ake ci da guminsu a ƙarshe ba wata diyya da ake ba su. Muhimmin abu a gareshi shi ne a mayar da hankali wajen kare haƙƙinsu maimakon a yi batun izinin zama cikin ƙasa.

Ya ce: "Bai kamata a yi fatali da ´yancin mutum ba saboda kasancewarsa baƙon haure ne ko ya karya dokar ƙasa ba. Ba daidai ba ne a danganta haƙƙin bil Adama da matsayin izinin zaman baƙo a cikin ƙasa."

A saboda haka shugaban cibiyar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rattaba hannu kan ƙudurin majalisar tarayyar Turai kan yaƙi da fataucin bil Adama, wanda aka tsara a shekara ta 2005.

Ban da azabar da suke sha a hannun ɓata gari, baƙin da ake ci da guminsu na kuma fama da matsaloli na zama cikin wani baƙon yanayi bayan sun yi ƙaura daga ƙasashensu na asali don ƙauracewa matsanancin hali na talauci.

Masallafa: Marcel Fürstenau/Mohammed Nasiru Awal

Edita: Zainab