Jamus da Indiya zasu karfafa ƙawancen su | Labarai | DW | 17.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Indiya zasu karfafa ƙawancen su

Jamus ta ce Ƙasar Indiya na da mahimmanci sosai wajen bunƙasar kasuwanni da siyasar ƙasar

default

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle.

Ƙasashen Indiya da Jamus waɗanda suka sami kujerun karɓa-karɓa a kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya a makon da ya gabata, za su ƙaddamar da wata tattaunawa daga gobe litinin domin neman sabbin hanyoyin gyare-gyare a Majalisar Ɗinkin Duniya, har da matsalar canjin yanayi da matakan tsaro, da ma dabarun yaƙi da ta'adanci. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya isa babban birini Indiya, wato New-Delhi a yau, inda zai gana da Frime Minista Manmohan Singh da ministan harkokin wajen Indiya Mr Mallaiah Krishna.

Kafin tafiyan dai Westerwelle ya faɗa wa manema labaru a nan Jamus cewa India na da mahimmanci sosai ga Jamus ba don bunƙasar kasuwanni kaɗai ba, amma har da bunƙasa a fannin siyasa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu