Jamus da harkokin tattalin arziki | Siyasa | DW | 09.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus da harkokin tattalin arziki

Karuwar fitar da kayayyakin da aka sarrafa a Jamus zuwa ketare

default

Michael Hüther

Sakamakon dogaro da takeyi kan fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen ketare, ya sanya Jamus take fuskantar matsanancin yanayi na tattali daga matsalar tattalin arziki, fiye da sauran ƙasashen Turai.

A yanzu haka dai kusan rabin dukkan kayayyakin da ake sarrafa a nan tarayyar Jamus ne ake fitarwa zuwa ƙasashen ketare. Kuma bisa dukkan alamu hakan lamarin zai cigaba da kasancewa, inji sabon nazari da cibiyar nazarin harkokin tattalin arziki ta Jamus dake birnin Köln tayi. A kusan ko'ina a sassa na duniya akwai bukatun mayar da hankali wajen manyan wuraren zuba jari, inji Direktan cibiyar nazarin harkokin tattalin Michael Hüther...

"yace matsalar da muke fuskanta a dukkan yankuna na duniya shine, yawan kuɗaɗen ajiya sunfi kuɗaɗen zuba jari yawa. Hakan yafi karfi a yankin gabas ta tsakiya da ƙasashen da suke da 'yancin kan zuwa yankin Asia"

A shekaru masu gabatowa dai za a daɗa samun karuwar yawan jama'a, musamman a kasashen dake tasowa, dama birane.Hakan na nufin nan da shekara ta 2050, za a samu karin yawan tsofaffi da kusan ninki uku. Acewar Hüther Jamus ta na kyakkyawan tanadi wa wannan yanayi.....

" yace waɗannan batutuwa ne da suka kunshi bukatu na harkokin tattalin arziki, zuba jari a harkokin ilimi, kiwon lafiya da fasahar kimiyya ta hanyar amfani da kayayyakin gargajiya.Waɗannan dukkan batutuwa ne da za a iya cewar sun ta'allaka akan tattalin arzikin Jamus, da kuma irin nasarorin da aka samu a 'yan shekarun da suka gabata"

Kazalika Direktan cibiyar nazarin tattalin arzikin na Jamus Michael Hüther yace, duk da karuwan bukatu na yau da kullum da kuma sauyin yanayi da duniya take fuskanta, ba za a kwatanta Jamus tafi sauran kasashe ba musamman a ɓangaren fasaha na zamani, da sabbin dabarun makamashi da take dasu.Sai a waje guda kuma ba a kyakkyawan mahawara dangane da karuwan kayayyakin da ake fitarwa zuwa waje ba.

" Michael ya ce, an samu nasarar karin fitar da kayyayakin da aka sarrafa zuwa waje, saboda suma a bangaren su ma'aikatan dake aiki a masana'antun suna samun kyakkyawan biya daidai gwargwado. Wanda hakan ne zai yi sanadiyyar karuwar gasa wajen farashin kayyaki , kana a ɓangare guda kuma ya durkusar da bukatun jama'a"

Dangane da haka ne ake samun karuwar fitar da kayayyakin masan'antun daga nan Jamus zuwa ketare. Sai dai dayake ana biyan ma'aikatan kamfanonin kudade daidai gwargwado, hakan ya haifar karuwar ayyuka, da kuma damar kashe kudade.

Mawallafiyya: Zaimanab Mohammed

Edita: Ahmad Tijani Lawal