1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

150110 Rüstungsexporte Deutschland

January 18, 2010

Jamus tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a faɗin duniya, amma ta gindaya sharuɗɗa masu tsauri kafin ba da izinin

https://p.dw.com/p/LYsx
Hoto: Anna Kuhn-Osius

A birnin Augburg na nan Jamus an fara shari´ar Karlheinz Schreiber, dillalin makamai, da ake zargi da ƙauracewa biyan haraji da ba da cin hanci. A cikin shekarun 1990 Schreiber ya ba da hanci ga jami´an Jamus ciki har da sakataren ƙasa na ma´aikatar tsaro, Ludwig-Holger Pfahls domin samun izinin sayarwa ƙasar Saudiyya da makaman yaƙi. Ko da yake Jamus tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a faɗin duniya, amma ta gindaya sharuɗɗa masu tsauri kafin ba da izinin.

Ana iya cewa jiya ba yau ba ga masana´antun ƙera makamai na Jamus. A cikin shekaru biyar da suka wuce yawan makamai da ƙasar ke sayarwa ƙetare ya ninka sau biyu, kamar yadda cibiyar nazarin batutuwan da suka shafi zaman lafiya ta birnin Stockholm wato SIPRI a taƙaice ta nunar. To sai dai Otfried Nassauer na cibiyar musayar bayanai kan al´amuran tsaro dake birnin Berlin, ya ce da wuya a iya sanin taƙammamen waɗannan alƙalumman.

"A cikin shekaru biyu da suka wuce tarayyar Jamus ta ba da takardun izinin sayar da makamai ƙetare da kuɗinsu ya kai Euro miliyan dubu tara. To sai dai hakan baya nufin an sayar da makamai na wannan adadi. Abin da ake magana kai shi ne na izini. To amma ko shakka babu Jamus na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya da suka fi sayar da makamai ƙetare. Sanin matsayinta a jerin waɗannan ƙasashe ya dogara ga ƙididdigar da aka yi amfani da ita."

Akan haka a kullum Jamus na shan suka domin a jerin masu sayen makaman har da ƙasashe dake cikin rigingimu kamar Pakistan da Isra´ila, waɗanda a shekarun baya-bayan nan suka kasance sahun gaba wajen bawa masana´antun Jamus ƙwangilar sayen jiragen ruwan yaƙi na ƙarƙashin teku. A kowace shekara babban taron coci kan raya ƙasa na ba da rahoto dangane da sayar da makamai ƙetare. Fada Karl Jüsten na majami´ar Katholika ya yi suka kan yadda Jamus ke sayar da makamai ƙetare.

"Duk mai son ya magance yaɗuwar makamai a yankuna kamar Gabas Ta Tsakiya, ko kudu da kudu maso gabacin Asiya ko kudancin Amirka, to bai kamata ya shiga cikin hada-hadar sayar da makamai ba."

Sai tare da cikakken izini ne kaɗai za´a iya fitar da makaman yaƙi kamar tankokin yaƙi da manyan bindigogi zuwa ƙetare. Amma ƙananan kayan aiki da ba za a iya amfani da su kai tsaye a matsayin makamai ba, wato kamar injunan jiragen ruwa, dokokin su na da ɗan sassauci. Akwai dai sharuɗɗa da dama da suka danganci ba da izinin sayar da kayaki ƙetare, ciki har da abin da za a yi da su, halin da ake ciki a ƙasa, shin waɗannan kayakin ka iya rura wutar rikici ko kuma ana iya amfani da su wajen take haƙin ɗan Adam? Dole sai an fayyace waɗannan tambayoyin, kamar yadda ake nema a yi a shari´ar da akewa dillalin makaman na Jamus Karlheinz Schreiber da harkar cinikin da ta haɗa shi da gwamnatin Helmut Kohl a shekarun 1990.

Idan aka kwatanta da sauran ƙasashen duniya Jamus na cikin waɗanda ke tsauraran dokokin sayar da makamai ƙetare. Duk da cewa ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai su amince da amfani da dokoki na bai ɗaya dangane da fid da makamai ƙetare amma ana samun banbanci wajen ba da izini tsakanin ɗaiɗaikun ƙasashen ƙungiyar.

Mawallafa: Matthias Bölinger/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi